1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haiti: An kwashe wakilan Amirka daga wurin jana'iza

Ramatu Garba Baba
July 23, 2021

An yi gaggawar kwashe wakilan kasashen yamma bayan da rikici ya barke a yayin da ake gudanar da jana'izar Shugaba Jovenel Moise da wasu 'yan bindiga suka halaka.

https://p.dw.com/p/3xxhv
Haiti Cap-Haitien | Beerdigung von Jovenel Moise: Unterstützer des ehemaligen Präsidenten fordern Gerechtigkeit
Hoto: Matias Delacroix/AP/picture alliance

Duk da tsauraran matakan tsaro da aka dauka, bai hana masu zanga-zanga kutsawa cikin taron gudanar da jana'izar Jovenel Moise shugaban kasar Haitin da wasu 'yan bindiga suka harbe har lahira a farkon wannan watan Yulin ba. Karar harbe-harben bindiga da aka zargi 'yan sanda da harbawa a cikin dandazon jama'a, ya haifar da rudani.

Magoya bayan shugaban, sun zargi manyan jami'an gwamnati kasar ta Haiti da hannu a kisan shugaban, wasunsu dauke da alluna masu rubuce-rubuce, sun diga ayar tambaya kan dalilan da suka hana irin rundunar da aka jibge wurin jana'izar iya tsare rai da lafiyan Shugaba Moise.

An dai yi gaggawan kwashe wakilan gwamnatocin Amirka dana Majalisar Dinkin Duniya da sauran da suka halarci jana'izar a sakamakon yamutsin. Uwargidan marigayin a yayin bankwannan karshe ga mijinta ta nemi a dauki mataki na ganin an yi adalci a gano wadanda suka aikata kisansa.