1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabashin Ukraine ya sake shiga rudani

Yusuf BalaJuly 27, 2015

Biyu daga cikin motocin masu sanya idanun daga kungiyar OSCE sun kama da wuta bayan da wasu makaman roka da gurneti suka fada musu.

https://p.dw.com/p/1G5FP
Ukraine, Militärmanöver Saber Guardian
Hoto: DW/H. Stadnyk

Gwamnatin kasar Ukraine ta bayyana cewa 'yan aware sun bude wuta kan fararen hula a gabashin Ukraine, a wani hari da ya ritsa masu sanya idanu daga kungiyar hadin kan tsaro ta kasashen Turai OSCE.

Biyu daga cikin motocin masu sanya idanun daga kungiyarr ta OSCE sun kama da wuta bayan da wasu makaman roka da gurneti suka fada musu a daidai lokacin da suke kan hanyar tsallakwa daga bangaren garin Luhansk na 'yan awaren zuwa bangaren da dakarun sojan gwamnatin Ukraine ke da iko da shi.

A cewar kungiyar tun da fari dukkanin bangarorin biyu sun amince da shirin tsallaka iyakokin da kungiyar ta OSCE ta gabatar musu.

A cewar kungiyar ta OSCE da ke sanya idanu kan rikicin na 'yan aware da dakarun sojan Ukraine ta ce bangaren sojan mahukuntan birnin Kiev su suka fara bude wuta.