Rikici ya kunno kai bayan bacewar kaya a hukumar zaben Ghana
March 20, 2024Na'urorin tantancewar ta biometric guda bakwai ne suka bata daga hannun hukumar zabe a kasar ta Ghana, al'amarin da 'yan adawar ke cewa ba lallai ba ne a tabbatar da sahihancin zaben shugaban kasa na bana idan ba a warware wannan matsala ba.
Hakan ya bayyana ne a cikin bayanan shugabar hukumar zaben a majalisar dokoki. Ana amfani da na'urorin ne wajen tantance sahihance masu zabe wadanda aka dauki bayanansu a lokacin yin rajista, kuma da hakan ne ake iya tantance duk mai kada kuri'a a ranar babban zabe.
A kan jadadda batan na'urorin har guda bakwai ne jagoran bangaren adawar gwamnati a majalisar dokokin kasar Cassiel Ato Forson, yake cewa da walakin.
''Ina rokon hukumar binciken manyan laifuka da hukumar ‘yan sanda ta kasa, su fidda sanarwa a take dauke da cikakkun bayanai a kan inda ake kai a bincikensu kawo I yanzu''
Tun bayan kama aikin Malama Jean Mensah bayan ta gaji Charlotte Osei a matsayin shugabar hukumar zaben Ghana ne dai, ake ta samun kananan maganganu a game da tafiyar da ayyukan hukumar zaben kasar.