1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai ta shiga rikicin bakin haure

Barbara Wesel | Lateefa Mustapha Ja'afar SB
November 17, 2021

Harkokin jinkai sun sukurkuce kan dubban bakin haure masu neman shiga kasashen Turai ta Poland daga kasar Belarus.

https://p.dw.com/p/436r0
Belarus Polen Mirgranten im Grenzgebiet
Hoto: Leonid Shcheglov/BelTA/AP/dpa/picture alliance

Har yanzu an gaza samun mafita a siyasance, kan yadda za a yi da 'yan gudun hijira da bakin hauren da ke jibge a kan iyakar Poland da Belarus a kokarinsu na shiga kasashen nahiyar Turai. Rahotanni sun nunar da cewa wani matashi ya rasa ransa, a daidai lokacin da sanyin hunturu ke kara yin tsanani. Tuni dai aka yi jana'izar matashin mai suna Ahmad al Hasan mai shekaru 19 da haihuwa cikin alhini, a kauyen Bohoniki da ke dab da kan iyakar Kuznica a kasar Poland, yankin da Musulmi masu tafiya fatauci ke cikinsa tun karni na 17.

Belarus - Polen | Beisetzung von Ahmad
Hoto: Wojtek Radwamski/AFP

Ba dai Ahmad al-Hasan ne kadai matashin da ya rasa ransa ba, akwai ma wani matashi daga yankin Kurdawa na kasar Iraki. Shi dai al-Hasan ya fito daga birnin Homs na Siriya, kasar da yaki ya daidata kuma ya tilasta dubban al'ummarta yin gudun hijira. Wannan matashi dai, ya fito ne daga sansanin 'yan gudun hijira da ke kasar Jordan. Kamar sauran 'yan uwansa da ke wannan sansani, sun karanta a kafafen sada zumunta na zamani cewa akwai hanyar shiga kasashen Tarayyar Turai EU ta birnin Minsk fadar gwamnatin kasar Belarus cikin sauki. Al Hasan na fatan kammala karatunsa na koyon sana'a, domin samun abin da zai gina rayuwarsa. Kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU dai, na zargin gwamnatin Shugaba Alexander Lukashenko ta Belarus din da bayar da wannan labari na kanzon kurege da ya isa kunnuwan dubban mutane daga yankin Kurduwa na Iraki da Siriya da kuma Afghanistan da ke neman shiga Turai da sukewa kallon tudun mun tsira.

Belarus Grenze zu Polen | Migranten | Zuspitzung der Lage
Hoto: Leonid Shcheglov/BelTA/AP/picture alliance

Al'ummomin da ke zaune a kusa da kan iyakar dai, a shirye suke su taimaki bakin hauren da ke yashe kara zube cikin sanyi. Kamar a kauyen na Bohoniki, ana tattara kayan sanyi da abinci domin agaza musu. Sai dai kadan ne daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Poland ke bayar da agaji a boye a wannan yankin. Ba za su iya karasawa kan iykara ba, kasancewar duk wanda ya fada hannun jami'an 'yan sandan na kan iyakar kashinsa ya bushe. Suna taimakwa 'yan gudun hijirar da bakin hauren da za su iya bayyana inda suke ta hanyar amfani da wayoyin hannun na salula, idan suna neasa da kan iyakar. Rahotanni sun nunar da cewa abu na farko da 'yan sandan na kan iyaka ke yi shi ne karbe wayar 'yan gudun hijirar, kamar yadda Agata Kolodziej daga kungiyar bayar da agaji ta "Ocalenie." A cewarta tana cike da alhini kuma abin takaici ne ganin yaddad jami'an tsaron ke hanasu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A yanzu haka dai, ra'ayoyin al'ummar kasar Poland din kan 'yan gudun hijira ya banbamta. Yayin da kaso sama da 50 cikin 100 ke ganin korarsu da jami'an tsaron kan iyakar ke yi daidai ne, sama da kaso 60 cikin 100 kuma na ganin ya kamata a bai wa 'yan gudun hijira damar neman mafaka.