1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Gabas ta tsakiya

July 17, 2006
https://p.dw.com/p/BuqJ

Shugabanin ƙungiyar ƙasashe masu cigaban masanaántu na duniya G8 a ƙarshen taron su a birnin St Petersburg na ƙasar Rasha, sun bukaci Israila da yan Hizbullah su gaggauta kawo ƙarshen hare haren da suke kaiwa juna ba tare da jinkiri ba. Shugabanin ƙasashen Britaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Rasha da kuma Amurka sun gabatar da matsayi na bai ɗaya dake buƙatar dukkan bangarorin su tsagita wuta. Bugu da ƙari sun yi kira ga Israila ta dakatar da farmakin soji da take yi a Gaza. Shugabanin ƙungiyar ta G8, sun kuma yi kira ga Majalisar ɗinkin duniya ta tura jamián tsaro na ƙasa da ƙasa domin nazarin halin da ake ciki a Lebanon. Nan gaba kaɗan a yau ministocin harkokin waje na ƙungiyar tarayyar turai za su gudanar da taro a birnin Brussels domin tattauna rigingimun da suke tasowa a gabas ta tsakiya. Jamiín tsare tsaren harkokin wajen ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana a jiya lahadi ya gana da P/M Lebanon Fuad Siniora. Shima jakadan majlisar ɗinkin Vijay Nambiar wanda ya jagoranci tawaga ta mutane uku ya tattauna da P/M na Lebanon inda ya buƙaci sakin sojojin da Hizbullah suka yi garkuwa da su da kuma buƙatar Israila ta dakatar da buɗe wuta a kan fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba. A halin da ake ciki gwamnatoci ƙasashe na duniya na ƙoƙarin kwashe alúmomin su daga ƙasar Lebanon a yayin da faɗa ke ƙara yin tsamari tsakanin Israila da Lebanon. A farmakin da Israila ta kai da jiragen sama da sanyi safiyar yau, ta ragargaza maájiyoyin mai guda biyu da suka rage a birnin Beirut kusa da filin saukar jiragen sama na ƙasar. Dama dai tuni Israilan ta yi luguden wuta a filin jirgin saman wanda ya kassara sauka da tashin jirage, abin da kuma ke ƙara haifar da matsanancin hali ga mutane dake son barin ƙasar waɗanda suka haɗa da baƙi yan ƙasashe ƙetare. Amurka ta fara kwashe yan ƙasar ta dake zaune a Lebanon yayin da ƙasashen Britaniya da Faransa da Rasha suma ke shirin kwashe na su alúmomin.