Rikicin gabas ta tsakiya
July 4, 2006Prammista Ehud Olmert, ya yi watsi da batun tantanawa da gungun palestinawan da su ka yi garkuwa da soja ɗaya na rundunar Israíla, tun ranar 25 ga watan da ya wuce.
Ya ce ko kussa ba za shi taba hawa tebri guda ba, da yan ta´ada.
A maimakon hakan, Isra´ila za ta yi iya ƙoƙarin ta, domin belin Gilad Shalit ta ko wace hanya.
Amincewa datantannawar, wata kafa ce,ta nuna goyan baya ga ta´adanci, inji Praminista Olmert.
Ƙasar Masar da ke shiga tsakanin wannan taƙƙadama ta yi kira ga shugaban Hamas Michael Khalid, da ke gudun hijira a Syria da ya umurci dakarun sa, su sallami wannan soja, muddun ba haka ba, Masar zata hidda hannuwan ta daga cikin al´amarin.
A nasu gefen, maharan sun lashi takobin ci gaba da tsare shi, muddunn Israela ba ta sako dubunan Prisinoni ba, Palestinawa da ta ke tsare da su a gidajen yari daban-daban.