1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ganduje da sarki: Buhari ya sa baki

June 19, 2019

Bayan tsawon lokaci ana takaddama daga dukkan alamu an kama hanyar gano bakin zaren warware rikici tsakanin gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma sarki Kanon Mallam Muhammad Sunusi na biyu.

https://p.dw.com/p/3KhrY
Nigeria neuer Emir von Kano Sanusi Lamido Sanusi
Hoto: Amino Abubakar/AFP/Getty Images

An kai har ga barazanar tsigewa an kuma kirkiro karin masarautu duk dai a cikin rikicin da ya shiga tsakanin gwamnan kano da kuma sarkin na Kano. Duk da cewar dai har yanzu ana kotu sannan kuma ita ma hukumar yakin hanci ta jihar na kara matsin lamba, daga dukkan alamu ana shirin ganin sauyin matsayi a bangaren manyan jami’an biyu na jihar.

Bayan wata ganawa da shugaban kasa dai gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yace an kama hanyar fahimtar juna a tsakaninsa da sarkin. Duk da cewa gwamnan bai fito fili ya baiyyana matakan da suka kai ga nasarar da yake ikirarin an samu ba, majiyoyi sun ce tun kafin ganawar tasa da shugaban kasar wasu jami’ai a fadar shugaban kasar karkashin jagorancin gwamnan Ekiti Kayode Fayemi sun nemi kai karshen rikicin a bangaren gwamnan.

Sai dai kuma Gandujen yace abun da ya dauki hankalinsa da shugaban kasar bai wuci maganar rashin tsaron da ta mamaye makwabtan jihohi ba wanda kuma ke neman yiwa jiharsa ta kano garkuwa daga matsalar ta yan ina da kisa. Tuni dai rikicin ya yi raba kan ‘yan bokon Jihar da su kansu masu sararutar dama ragowar jama’ar jihar sannan kuma ke neman yin tasiri ga makomar tattalin arziki da siyasa a jihar.