1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Israila da Gaza an kasa tsagaita wuta

May 19, 2021

Shugabannin kasashen duniya sun bukaci tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas sai dai kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kaza cimma matsaya kan sanarwar da zai fitar.

https://p.dw.com/p/3td2v
Israel - Palästina-Konflikt
Hoto: Said Khatib/AFP/Getty Images

A wannan laraba Israila ta cigaba da luguden wuta a Gaza yayin a nasu bangaren Hamas ke cigaba da harba rokoki zuwa cikin Israila.

Sojojin Israila sun ce sun kai hari kan wasu cibiyoyi a Khan Younis da Rafah inda jirage 52 suka kai hari cibiyoyi 40 cikin mintuna 25.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito cewa mutane shida sun rasu a wani hari ta sama da Israila ta kai yayin da wasu hare haren sula lalata wani gini mai dauke da iyalai 40 a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Hare haren na zuwa ne kwana guda bayan da Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kammala taro kan rikicin na Israila da Gaza ba tare da wakilan kwamitin 15 sun cimma matsaya kan sanarwar da za su fitra ba.