Rikicin kudin euro a ƙasashen Girka da Belgium
June 18, 2011Shugaban rukunin ƙasashe masu amfani da kuɗin bai ɗaya na euro Jean Claude Juncker ya yi kashedi a yau asabar cewa rikicin kuɗin da a yanzu ya dabaibaye ƙasar Girka ka iya shafar ƙasashen Belgium da Italiya. Juncker wanda har ila yau shine Firaministan ƙasar Luxembourg da kuma ke jagorantar ministocin kuɗi na ƙasashe masu amfani da kuɗin na euro ya shaidawa jaridar Süddeutsche Zeitung ta nan Jamus cewa matsalolin kuɗin sun tilastawa ƙasashen Girka da Ireland da kuma Portugal neman ceton gaggawa. Juncker har ila yau ya yi gargaɗin cewa kada a yi gaggawar neman kafofin kuɗaɗe masu zaman kansu shiga cikin shirin ceton da za'a baiwa Girka ya na mai cewa yin hakan na iya bada kafar taurin bashi wanda kuma ke da mummunan sakamako ga kuɗin na euro.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal