1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kudin Girka na daukar sabon salo

November 2, 2011

Majalisun Girka sun bada goyon bayansu ga shugaba Papandreou wajen ganin an kada kuri'ar raba gardama dangane da tallafin da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin basu

https://p.dw.com/p/133VA
Frime Ministan Girka George PapandreouHoto: AP

Majalisar ministocin Girka ta amince ta goyi bayan shirin Frime Ministan kasar George Papandreou na gudanar da kuri'ar raba gardama dangane da yarjejeniyar tallafin da suka cimma tare da Kungiyar Tarayyar Turai. Kakakin gwamnatin kasar ya yi wannan sanarwar ne a birnin Athens bayan da ministocin suka shafe sao'i bakwai suna ganawa. Wasu daga cikin ministocin sun ce sun soki lamirin Papendreou domin kiran da yayi da a kada wannan kuri'ar raba gardamar, amma sun amince su goyi bayan tayin gabanin kuri'ar neman goyon bayan majalisar dokokin da za'a jefa ranar Juma'a mai zuwa.

Wannan sanarwar jefa kuri'ar da Papandreou ya yi ranar litinin dai ya zo wa jamiyyar sa ta Socialist Party cikin bazata, a yayinda wasu kasashen turan ma kamar Burtaniya ke cigaba da nuna mamakin su dangane da wannan mataki da Girkan ke shirin dauka, kamar yadda Sakataren harkokin wajen Burtaniyan William Hague ya bayyana

" Lallai mun ji mamaki, manyan biranen Turai sun ma yi mamaki sosai, ko daya bamu zaci zasu yanke wannan shawarar ba. Kuma a ganinmu yana da mahimmanci duk kasashen da suka kasance a wannan yarjejeniya da aka cimma dangane da rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro a makon da ya gabata, da su aiwatar da ita amma mafi mahimmanci shine wannan abu ne da ya shafi Girka da siyasarta na cikin gida".

Mawallafiya: Pinado Abdu        

Edita          : Umaru Aliyu