1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kuɗin Girka ya mamaye taron G20

November 3, 2011

Ƙasashe G20 da suka fi ƙarfin masana'antu na nazarin hanyoyin da ya kamata su bi wajen mayar da tattalin arzikin duniya kan kyakkyawar turba.

https://p.dw.com/p/134X5
Shugabannin G20 sun gudanar da taron share fage kafin na ƙoli.Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabannin ƙasashen 20 da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya sun gabatar da taron ƙolinsu na yini biyu a birnin Cannes na ƙasar Faransa, da nufin laluɓo bakin zaren warware rikicin kuɗi da ke addabar wasu sassa na duniya. Wannan dai shi ne karo na shida da ake gudanar da irin wannan taron ƙoli, tun bayan wargajewar bankin zuba jari na Lehman Brothers a ƙasar Amirka shekaru uku da suka wuce, wadda ke zama ummal aba'isan wannan rikicin.

 Shugaban Faransa Nicolas sarkozy da kuma takwaransa na Amirka Barack Obama sun tattauna tsakaninsu gabanin buɗe taron, da nufin cimma matsaya game da hanyoyin da ya kamata a bi domin shawo kan matsalar ta tattalin arziki. Ita dai faransa da ke shugabantar ƙungiyar ta G20 ta na neman ƙasashen yammacin duniya su haɗa karfi da ƙasashen da ke samun bunƙasar arziki irin su china da Indiya wajen magance wannan rintsi na koma bayan arziki.

Daga cikin batutuwan da za su mamaye wannan taron, har da raɗaɗin koma baya da Girka ta sami kanta ciki da kuma hanyoyin tsamota daga wannan hali.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu