Rikicin makaman nuklear Iran
May 8, 2006Nan gaba a yau ne, ministocin harakokin waje na ƙasashe 5 masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, wato Amurika, France, Rasha, Britania da China, za su sake komawa tebrin shawara, a birnin New York na Amurika, domin ci gaba da tantanawa, a game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran.
Taron zai samu halartar ministan harakoki wajen Jamus da sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamaya turai Havier Solana.
A wani dandalin kuma na daban, ƙasashe 15 membobin a komitin sulhu, za suyi wani taron, wanda shima ya ta´alaƙa a kan wannan badaƙala.
Tarrurukan guda 2,za su mahaurori a kan shawarwarin da ƙasashen France, Amurika, da Britania su ka gabatar as makon da ya gabata,inda su ka zayyana hanyoyi da atunanin su kan iya magance rikici.
A taiƙaice, shawarwarin sun ƙara kira ga Iran, ta bi umurnin Majalisar Ɗinkin Dunia, wato ta yi watsi da aniyar ta, na ƙera makaman ƙare dangi.
Saidai har ya zuwa yanzu kasashen Rasha da China dage goyan bayan Iran an nuna adawa ga taswira da ƙasashen 3 su ka gabatar
A dangane da tarurukan jikadan Amurika a Majalisar Ɗinkin Dunia John Bolton na mai cewa
Mu na duba hanyoyin cimma yarjejeniya ta bai ɗaya da zata samu amincewa daga membobin komitin sulhu baki ɗaya, wada kuma zata kasance wata ƙwaƙwara alama ga Iran, don ta gane cewar ƙasashen fa sun ɗaura aniyar cimma buri.
A nasa ɓangare sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Koffi Annan, ya shawaraci mahalata taron da su yi hurhuren ciwo kan Iran, da wasu mattakai masu kwaɗaitarwa, wato kamar irin abinda hausawan kance, tarkon angullu sai da kashi.
Annan ya ce:
Ya wajabta, mu tantana a kan hanyoyin baiwa Iran inganttatun husa´o i´na zamani, da kuma tabbatacen tsaro,
a tunani na, ya na da kyau ,a hau tebrin shawara tsakanin Amurika ƙasashen turai, Rasha da Iran, domin gano bakin zaren warware rikicin cikin ruwan sanhi.
To a wani mataki irin na ba zata, shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinejad, ya rubuta wasiƙa zu ga shugaba Georges Bush na Amurika.
Kakakkin fadar shugaban Iran Gholam Hossein Elham,da ya yaɗa wannan labari yau, ya sanar cewa, wasiƙar na ƙunshe da shawarwarin Iran na magance rikicin.
Kazalika, a cikin wasiƙar Mahamud Ahmadinedjad, ya yi nazari a game da rikice- rikicen da ke barkewa a dunia, a halin yanzu, da kuma matakan bi, domin kawo ƙarshe su.
Tun shekaru 26 da su ka gabata, a ka kaste huɗoɗin diplomatia, tsakanin Iran da Amurika, a duk tsawan wannan lokaci, wannan shine karro na farko, da wani shugaban ƙasar Iran, ya rubuta wasiƙa zuwa shugaban ƙasar Amurika.
Wasiƙar za ta bi ta hannun jikadan ƙasar Suizland a birninTeheran da ke wakiltar Amurika.