1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin makamin nukiliya na Iran..Russia tace ba da ita ba

April 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1C

Kasar Russia ta tabbatar da cewa ba zata yarda da matakin sakalawa kasar Iran takunkumi ba a game da kace nacen da ke wakana na aniyar kasar mallakar makami na nukiliya.

A cewar ma´aikatar harkokin wajen kasar , Russia zata amince ne da matakin sawa Iran takunkumi ne kawai, matukar an gabatar mata da gamsassun hujjoji cewa nukiliyar da take kokarin kerawa na tayar da zaune tsaye ne.

Wadan nan kalamai na Russia sun biyo bayan irin yadda Amurka ta dage akan neman goyon bayan kasashe masu zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd ne , na neman su rufa mata baya don daukar matakin ladaftarwa akan kasar ta Iran.

Tuni dai Mdd ta tabbatar da cewa babu wasu gamsassun hujjoji dake tabbatar da cewa kasar ta Iran na kokarin mallakar makami na nukiliya ne.

Haka a waje daya ita kanta Iran tasha nana ta cewa nukiliyar ta ta zaman lafiya ce , amma bata tashin hankali ba kamar yadda kasashen yamma ke zato.