Rikicin makiyaya da manoma ya yi tsamari a Nijar
October 28, 2016A yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar daruruwan manoma ne suka tashi a tutar babu sakamakon mamayar gonakin noma da garke-garke daga makiyaya a karamar gundumar Damagaram Takaya, Tuni dai hukumomi suka kame dabbobin makiyayan da suka aikata barnar don rama cimakar da dabbobin suka ci. Wanan barna dai ta zo kafin hukumomi su bada wa'adin sakin gonakin noma a hukumance.
Wanan halin tsaka mai wuya dai ya ritsa ne da manoman karamar gundumar Takaya daya daga cikin kananan gundumomi goma na baya-bayan nan sabbin girkawa a yankin Damagaram. Wasu manoma na barin 'ya'yansu su kwana a gonaki saboda tsaro.
To sai dai a cewar daya daga cikin matan makiyaya da ta ki amincewa a dau muryarta ta na kokarin tattara dabbobin da suka watsu a gona ba su da zabi biyayya suke wa mazajensu.
Hukumomi sun kame dabbobi masu yawa da suka hada da tumaki da shanu a wani mataki na biyan diyya ga manoman. Har izuwa lokacin hada wanan rohoto dai kokarin da wakilin DW a Damagaram ya yi don jin ta bakin wakilan makiyaya hakarsa ba ta cimma ruwa ba.