1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Nuclearn Iran

May 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6f
Kasashen Amurka da Britania da Faransa sun kammala shirin gabatarwa komitin sulhun mdd ,kwarya kwaryar kudurinsu,wanda zai bawa iran wata dama na dakatar da shirin nucleanrta.-To sai dai bisa dukkan alamu ,manyan kasashen yammaci bazasu gabatarwa Rasha da Sin wannan kuduri nasu ba,sakamakon adawa da suka bayyana da matakan.

Moscow da Beijing dai na ganin cewa wanann wani mataki ne daya doshi kakabawa Iran takunkumi ko kuma amfani da karfin soji akanta.Jakadan Amurka a mdd John Bolton ya fadawa taron manema labaru cewa zasu bayyana komitin matsayinsu da kuma matakin daya dace a dauka akan Iran.Wannan ganawar ta mdd wadda zata gudana a yau dai,yazo daidai da ganawar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,da shugaba George W Bush na Amurka a birnin Washinton ,adangane da batun nuclearn Iran.Jamian jamus din dai sun bayyana cewa Angela Merkel zatayi kokarin kira ga Bush dayayi taka tsantsan da batun Iran,domin kada a sa mu rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen turai,kamar yadda ya faru a kann Iraki.