1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliya na Iran

February 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuRQ

Shugaban hukumar kula da kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa,Muhammad El Baradei yace akwai yiwuwar cewa nan da watanni 6 zuwa 12 kasar Iran zata iya inganta sinadareb uraniyum mai yawa.

Kodayake shugaban hukumar ta hana yaduwar nukiliya yace zai dauki akalla shekaru 5 kafin kasar ta Iran ta iya kera makamin nukiliya.

Hakazalika Muhammad Al Baradei ya baiyana shakkunsa cewa da kyar Iran zata cimma waadin Majalisar Dinkin Duniya na ranar laraba domin dakatar inganta uraniyum.

Komitin sulhu na Majalisar dinkin duniya dai tuni ya lakabawa Iran takunkumi watanni biyu da suka shige,domin tilasata mata dakatar da shirin nata.

A yau ake sa ran El Baradei zai gana da wakilin Iran a tattaunawar nukiliyarta Ali Larijani.