1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar kasar Iran

Ibrahim SaniMay 31, 2006

Har yanzu tana kasa ta na dabo a game da kokarin da ake na warware rikicin nukiliyar kasar Iran

https://p.dw.com/p/Btzu
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai duk da irin kalaman da suke fitowa daga kasashen yamma na cewa,aniyar kasar Iran na mallakar makamin nukiliya baraza ce ga duniya, a karon farko shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato Mohd El Baradei yace ko kadan babu wata babbar barazana da wannan aniya ta Iran takewa duniyar.

A cewar shugaban hukumar ta IAEA, akwai bukatar bin wannan al´amari ta cikin ruwan sanyi don nemon bakin zaren warware shi ta hanyar diplomasiyyya, kin yin hakan a cewar Mohd El Baradei, ka iya haifar da sake kuskure irin wanda aka tafka a kasashen Iraqi da kuma koriya ta arewa.

A misali a cewar Mohd El baradei, anyi gaggawar daukar mataki akan kasar Iraqi a game da zargi da ake mata na mallakar wannan makami, sai daga baya kuma aka gano cewa bata dashi. El Baradei ya kara da cewa irin tashe tashen hankula dake ci gaba da faruwa a Iraqi a yanzu haka ya isa duniya darasi

A game da kasar koriya ta arewa kuwa anyi ta cece kuce ne na kokarin saka mata takunkumi, wanda hakan ya haifar da rashin jituwa a tsakanin ta da gamayyar kasa da kasa.

Bisa hakan a cewar Mohd El Baradei,hukumar da yakewa shugabanci wato IAEA na nan na ci gaba da bincike da kuma kokarin bin hanyar diplomasiyya wajen ganin an warware takaddamar dake tattare da wannan aniya da kasar ta Iran tasa a gaba.

A cewar shugaban hukumar ta IAEA, ya hakikance cewa da yawa daga cikin iraniyawa nada ra´ayin ci gaba da mu´amulla da sauran kasashen duniya.

Wannan jawabi dai na shugaban hukumar ta IAEA da alama ya samo asali ne a game da kokarin da kasar Amurka keyi na ganin lallai an sakawa kasar ta Iran takunkumi, wanda hakan ka iya mayar da ita saniyar ware a cikin gamayyar kasa da kasa.

Ci gaba da kurarin sakawa Iran takunkumi a cewar shugaban hukumar ta IAEA, ka iya hasala kasar ci gaba da mayar da martani, wanda hakan ba lallai ne yayiwa duniya dadi ba.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa har yanzu babu takamaiman bayanin cewa nukiliyar da kasar ta Iran take son kerawa ta zaman lafiya ce ko kuma ta tashin hankali, to sai dai mahukuntan kasar ta Iran sun sha fadin cewa nukiliyar da suke son kerawa ta bunkasa ci gaban kasar ce amma bata haifar da tsugune tashi ba.

A dai gobe alhamis idan Allah ya kaimu ake sa ran kasashe biyar din nan masu zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd tare da Jamus zasu gudanar da wani taro a birnin Vienna na kasar Austria, don ci gaba da duba hanyoyin warware wannan takaddama.

Ba a da bayan batun ihisani da ake tunanin bawa kasar ta Iran don dawowa daga rakiyar aniyar data sa a gaba, kasashen za kuma su duba batun ladaftar da kasar ta Iran idan ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu ga umarnin gamayyar kasa da kasa na daina sarrafa sanadarin ta na Uranium.