Rikicin nuklear Iran
September 2, 2007Shugaban ƙasar Iran, Mahmud Ahmadinedjad, ya gabatar da saban jawabi, a game da rikicin nukleya.
A cewar shugaban, a yanzu Iran ta mallaki a ƙalla cibiyoyin samar da makasahin nuklea dubu 3 a sassa daban-daban na ƙasa, sannan ba dare ba rana, masana ta fannin harakokin makamashi, na cigaba da bincike, don ƙara inganta wannan tashoshi, da kuma ƙirƙiro wasu sabi.
Wannan addadi ya saɓawa wanda hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta bayyana, cikin rahoton ta, na watan Ogust da ya wuce, wanda a ciki, ta nunar da cewa, Iran ta mallaki kussan tashoshi dubu 2.
Shugaba Ahmadinedjad ya ƙara jaddada matsayin ƙasar sa, na babu gudu, babu ja da baya, a game da batun mallakar makashin nuklea.
Kazalika, ya ƙalubalanci ƙudururukan komitin sulhu na majalisar Ɗinkin Dunia, wanda ke barazanar sakawa Iran takunkumin karya tattalin arziki, muddun ta ƙi bada kai bori ya hau ,a game da rikicin nukleya.