1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

rikicin Pakistan da Afghanistan

March 7, 2006

Ana fama da sabani tsakanin Pakistan da Afghanistan akan matakan yaki da ta'addanci

https://p.dw.com/p/Bu1G

Da kakkausan harshe kuma ba tare da amfani da wani salo na diplomasiyya ba, a ranar lahadi da ta wuce, shugaba Musharraf na Pakistan ya shiga sukan lamirin takwaransa na Afghanistan Hamid Karzai, a cikin wata hira da tashar telebijin Amurka ta CNN tayi da shi. Hakan ya kara tsaurara hali na dardar da ake fama da shi tsakanin kasashen biyu a ‘yan makonnin baya-bayan nan. A wata ziyarar da ya kai kasar Pakistan watan fabarairun da ya wuce shugaba Karzai ya mika wa Musharraf sunaye da cikakkun bayanai na mayakan Taliban a Pakistan, abin da ya hada har da tsofon shugaban Taliban Mullah Omar.

Ko da yake kasar Pakistan ta dakatar da dukkan taimakon da take ba wa Taliban bayan hare-haren nan na 11 ga satumban shekara ta 2001, amma jami’an siyasar Afghanistan har yau suna ci gaba zargin Pakistan da yin watsi da dandalin horar da dakarun Taliban din a harabar kasarta. A baya ga haka a ganin jami’an na Afghanistan sai tare da taimakon Pakistan ne kawai ‘yan Taliban ke da ikon ci gaba da hare-harensu na sare-ka-noke. A ziyarar da ya kai Pakistan a karshen makon da ya gabata shugaba George W. Bush yayi kira ga shuagabannin kasar da su kara yin hobbasa a matakansu na yaki da ta’addanci. To sai dai kuma a hirar da tashar CNN tayi da shi shugaba Musharraf ya mayar da martani da kakkausan harshe, inda yake cewar:

“Sun mika mana jerin sunayen mutane. Amma na yi mamaki matuka ainun a game da yadda labarin ya sulale a bainar jama’a. Tun da hakan ya faru, abin da zan ce shi ne mun yi bitar bayanan da aka ba mu, inda muka gano cewar kimanin kashi biyu bisa uku na bayanan tsofon labari ne. A ganina wannan wani yunkuri ne kawai aka yi domin shafa wa Pakistan kashin kaza. Shi kansa shugaba Karzai ba ya da wata masaniya a game da abin dake faruwa a kasarsa. Shawara daya da zan ba shi shi ne ya nemi tuntubar juna tare da hukumarsa ta leken asiri da ma’aikatarsa ta tsaro da kuma hukumar leken asirinmu.”

A lokaci guda shugaba Musharraf ya bayyana rashin jin dadinsa a game da gurbacewar yanayin dangantaku tsakanin Pakistan da Afghanistan. Amma a hakika, kamar yadda Conrad Schetter daga cibiyar nazarin manufofin raya kasashe masu tasowa dake nan birnin Bonn ya nunar ta dade tana kasa tana dabo a dangantakar Pakistan da Afghanistan kuma matsalar ta shafi kabilar Pashtu ce. Shetter ya kara da cewar:

“Wani abin lura shi ne yankin iyakokin kasashen biyu yanki ne na kabilu, wanda babu daya daga cikin kasashen dake da ikon katsalandan a cikinsa. A sakamakon haka shawo kan matsalar ya ta’azzara.”