Rikicin Pakistan
July 5, 2007Bisa ga dukkan alamu dai gwamnatin Pakistan ta kosa ne da matakai na tsokana da masu zazzafan ra’ayin addini dake bin salo na kungiyar Taliban ke dauka a daidai tsakiyar birnin Islamabad. A makon da ya gabata dalibai maza da mata dake koyan darussan addini a masallacin na lal-masjid, dake ma’anar jan masallaci sun dauki hankalin jama’a sakamakon wani matakin da suka dauka na kai farmaki kan katunan sayar da finafinan bidiyo da fayafayan CD, wai saboda musulunci ya haramta cinikin wadannan abubuwa, sannan suka shiga kame-kame da garkuwa da matan da suke ikirarin cewar wai karuwai ne da suka fito daga kewayen yankin, musamman ma ‘yan kasar China.
Kasar ta China, wadda bisa al’ada dake da alaka ta kut da kut da Pakistan, mai yiwuwa ita ce tayi matsin lamba akan fadar mulki ta Islamabad domin ganin ta kawo karshen wannan tabargazar dake faruwa gaban kofarta. Wani abin lura a game da wannan ci gaba na baya-bayan nan shi ne kasancewar duk wanda yayi bitar abin dake faruwa da idanun basira zai ga cewar musulmin masu zazzafan ra’ayi, wadanda ake kiransu ‘yan jihadi a Pakistan tuni suka zama saniyar ware a al’amuran siyasa da zamantakewa da kuma addini a kasar. Da yawa daga al’umar kasar na murna da farin cikin cewar nan ba da dadewa ba za a kawo karshen muzantawar da suke fuskanta daga lal-masjid. To sai dai kuma hakan baya nufin murkushe ayyukan ‘yan Taliban a kasar Pakistan. Muhimmin abin da ake bukata a yanzu shi ne gwamnatin kasar ta fito fili ta bayyana ainifin alkiblar da ta fuskanta, kada ta nemi yin amfani da rikicinta da ‘yan jihadin a gwagwarmayar kama madafun iko tsakaninta da ‘yan hamayya. Domin kuwa a cikin tarihin kasar na shekaru 30 da suka wuce, kama daga Zia-Ul-Haq zuwa yanzu, an lura da cewar gwamnatocin kasar su kan nemi fakewa da guzuma domin su harbi karsana inda suke amfani da kungiyoyi masu zazzafan ra’ayi na addini, wadanda su kansu ba su jituwa da juna domin murkushe ‘yan hamayya. A halin yanzu haka akwai masu tattare da imanin cewar gwamnati ta kirkiro wannan rikici ne domin ta samu kafar danne adawar da take fama da shi akan korar alkalin alkalan kasar Iftikhar Chaudhary da tayi. Muddin kuwa mutane na tattare da wannan ra’ayi da wuya ta samu goyan baya wajen tinkarar ‘yan tsagerar dake ta da zaune tsaye a kasar.