Rikicin shirin makamashin Nukiliyar Iran
December 7, 2010Har yanzu da sauran rina a kaba dangane da ƙokarin da ake yi na warware rikicin makamashin Nukiliyar Iran, bayan kammala taron yini biyu a birnin Geneva ba tare da cimma wata matsaya ba.
Manyan ƙasashe masu faɗa a ji da Iran din dai sun kammala tattaunawar ta birnin Geneva ne da yarjejeniyar sake zama a watan Janairu mai kamawa a birnin Istambul ɗin ƙasar Turkiyya.
Da yake tsokaci dangane da yadda ɓangarorin biyu suka yi hannun dangane da matsayinsu kan rikicin, shugaba Mahmoud Ahmedinejad na Iran, ya ce tattaunawa irin wannan zata cimma tudun dafawa ne kaɗai, idan har an cire takunkumin da ƙasashen suka kakabawa ƙasarsa. To sai dai manyan ƙasashen na muradin ganin an samu cigaba a tattaunawar kafin su ɗage takunkumin na su akan Iran. Akan haka ne Jami'ar kula da harkokin ketare na Ƙungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton ta ce Iran da manyan ƙasashen shida da ke ƙokarin warware wannan matsala ta hanyar diplomasiyya, za su sake ganawa a birnin Istanbul a ƙarshe watan Janairu domin domin shawo kan matsalar Nukiliyar ta Iran.
Sai dai babban Jami'in shiga tsakani na Iran a tattunawar Saeed Jalili ya ce Tehran ba zata amincewa matsin lamba ba.
Al'ummar ƙasar Iran din dai na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan hali da ake ciki.
Halin tattalin arziki da Iran din ke ciki dai shine ya jefa al'ummar kasar cikin halin kakanikayi dangane da rayuwarsu. Ana cigaba da fuskantar faduwar darajar kudi ga karuwar yawan marasa aikinyi musamman tsakanin matasa.
Wani matashi yace "a yayin da mutane suke fama da yunwa, kana matasa na cigaba da dogaro da shan miyagun ƙwayoyi, kana a hannu guda kuma gwamnati ta hana 'yancin walwalarmu, ban san amfanin menene amfanin makamashin Nukiliya a garemu ba".
Tarayyar Turai dai na shirya tattaunawa da Iran akan shirin Nukiliyarta amadadin manyan ƙasashe shida da suka kunshi Amurka, Rasha, China, Britaniya, Faransa da Jamus. Catherine Ashton ta jaddada cewar Manyan ƙasashen sun haɗa kai ne da nufin warware damuwar ƙasashen Duniya dangane da shirin Nukiliyar ta Iran.
A yayin taron na yinu biyu a birnin Geneva dai,ƙasashen sun yi ƙokarin tursasawa Iran ta amince da tattauna ayyukan Nukiliyarta, wadda ƙasashe yammaci ke wa zargin kera boma boman Atom.
Jami'ar EU ɗin dai ta bayyana tattaunawar tasu a matsayin wani matakin farko na samun nasara, kasancewar matsalar ba wadda za'a iya warwarewa cikin kwanaki biyu bane.
Shugabannin ƙasashen larabawa na yankin Gulf da ke gudanar da taro a a birnin Abu Dhabi, sun yi kira hukumomin Tehran da su amince da bukatun ƙasashe masu faɗa a ji, dangane da shirin Nukiliyar janhuyar Islamar mai sarƙaƙƙiyyar gaske. A cikin sanarwar haɗin gwiwa da suka gabatar ƙasashen kazalika sun yi maraba da kokarin ƙasashen Duniya wajen bin hanyar diplomasiyya a cimma sulhu kan batun.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal