Rikicin siyasa a Pakistan na ci gaba da tsamari
November 24, 2007Pakistan ta yi Allah wadai da matakin ƙungiyyar ƙasashe renon Ingila na dakatar da ita daga cikin ´ya´yan ƙungiyyar. Matakin a cewar Gwamnatin ta Pakistan, abune da bai dace ba , sakamakon rashin tushe . A takaice ma, Pakistan ɗin ta yi kurarin ficewa daga cikin ƙungiyyar ta Commonwealth, matuƙar ƙungiyyar ba ta ɗauki matakin gyara ba. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito babban sakataren ƙungiyyar ta Commonwealth Don Mackinnon na cewa ɗaukar matakan ya biyo bayan kunnen kashi ne da Pakistan ta nuna, bisa shawarwari da aka ba ta. Ƙungiyyar ta Commonwealth ta buƙaci Pakistan cire dokar ta ɓacin data kafa tare da sako fursunonin siyasa. An dai cimma matakin dakatar da ƙasar ta Pakistan ne, a taron kolin ƙungiyyar ta Commonwealth da a yanzu haka ke ci gaba da gudana a birnin Kampala na ƙasar Uganda.