1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Pakistan na daukar sabon salo

Ibrahim SaniNovember 17, 2007
https://p.dw.com/p/CINr

Mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka, Mr John Negroponte, ya bukaci Pakistan kawo karshen dokar ta ɓaci a ƙasar. Mr Negroponte ya faɗi hakan ne a lokacin ganawarsa da Mr Musharraf.A nan gaba ne ake sa ran wakilin na Amirka zai gana da shugabar adawa ta ƙasar, Benazir Bhutto. Pakistan ta faɗa rikicin siyasa ne, sakamakon dokar ta ɓaci da Mr Musharraf ya ƙaƙabawa ƙasarne.Ma su nazarin siyasa dai na kallon matakin shugaban ƙasar, a matsayin wata kaface ta dakushe harkokin Dimokruɗiyya, to amma Mr Musharraf ya musanta wannan hasashe:Mr Musharraf ya ce babu wata sarkaƙiya da dokar ta ɓaci za ta iya kawowa ga batu na gudanar da zaɓe mai tsafta, domin an kafa dokar ta ɓaci ne don inganta tsaro da oda a ƙasa, shi kuwa zaɓe mai adalci na tattare ne ingancin hanyoyin da aka gudanar da shi ne, a don haka kowanne zaman kansa ya ke.