1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar kasar Iran ya fara daukar sabon salo

May 25, 2006
https://p.dw.com/p/Buww

Kasar Iran da alama ta fara saukowa daga kujerarr nakin data hau na ci gaba da sarrafa sanadarin ta na Uranium.

A cewar shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato Mohd El Baradei, Kasar ta Iran ta amince ta dakatar da ayyukan ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium na tsawon wasu shekaru masu zuwa.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan wata ganawa ce data wanzu a tsakanin hukumar IAEA, da kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka wato CR.

A waje daya kuma, taron kasashe biyar din nan masu zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd tare da Jamus, sun nunar da cewa ana samun ci gaba dangane da kokarin da suke na samo bakin zaren warware rikicin nukiliyar kasar ta Iran.

Majiya mai karfi dai tayi nuni da cewa taron kasashe biyar din da kuma Jamus na kokarin binciko irin tallafi da kuma takunkumi da zasu sarkafawa kasar ta Iran ne don hana ta ci gaba da wannan aniya data sa a gaba.