Rikicin siyasar Kwango na kara kamari
September 20, 2016Rikicin wanda ke da nasaba da siyasa dai ya shiga kwanansa na biyu dai ya yi sanadin rasuwar mutane da dama. 'Yan adawa na kasar dai na bayyana rashin amincewa ne da abin da suka kira take-taken shugaba Kabila na neman tsawaita wa'adin mulkinsa bayan da gwamnatin ta ki bayyana jadawalin zabe wanda a bisa kundin tsarin mulki ya kamata a gudanar watanni uku kafin cikar wa'adin mulkin shugaban wanda zai kare a ranar 20 ga watan Disamba na wannan shekarar.
Masu adawa da tsawaita mulkin Kabila ciki kuwa har da sakataren babbar jam'iyyar adawa ta Union for Democracy UDP Felix Tshisekedi sun dora alhakin kisan da aka yi wa masu zanga-zanga a ranar Litinin din da ta gabata kan dakarun sojin kundunbala na gwamnati wadanda suka rika harbi na kan mai uwa da wabi. Kasashen duniya da ma Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da tashe tashen hankula da kuma kashe-kashen da suka biyo baya.
Wani abu da ake ganin ya ta'azzar halin da kasar ke ciki yanzu haka shi ne rushewar tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan adawa kan yadda za'a samo masalaha da kuma tsara jadawalin zaben kasar. Manyan shugabannin adawar sun kauracewa tattaunawar bayan da jam'iyya mai mulki ta bada shawarar yin gwamnatin hadin kan kasa zuwa zabe na gaba, amma Kabila zai ci gaba da kasancewa a kan mukamin shugaban kasar. Abin kuma da yan adawar suka ce ba za ta sabu ba.
Masu sharhi dai na ganin cewa lamarin da kamar wuya a sami wani shugaban da zai maye gurbin Kabila a wannan yanayin da ake ciki. Yanzu haka dai an zuba ido don ganin irin matakin da shugaba Kabila da kuma gwamnatinsa za su dauka cikin makonni masu zuwa ko ya Allah za su iya daidaita lamura ko akasin haka.