1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Pakistan

GwanduNovember 13, 2007
https://p.dw.com/p/CDUP
Tsohuwar Prain-Ministar Pakistan Benezir Bhutto, ta yi kira ga shugaba Pervez Musharraf da ya sauka daga kann mukaminsa na shugabancin kasar. Bhutto, ta yi wannan kiran ne, lokacin da take hira da ‚yan jaridu ta wayar talho daga birnin Lahore, inda take zaman daurin talala, matakin da gwamnati ta dauka domin hanata gudanar da zanga-zanga tare da magoya bayanta. Wannan shine karon farko da Bhutto zata fito fili, tana neman Musharraf ya ajiye mukaminsa na shugabancin Pakistan. Ko da yake gwamnati, ta sanar cewar ta dauki wannan mataki na daurin kawnaki bakwai kann tsohuwar Prain-Ministar, domin kare ta daga ‚yan ta’adda masu neman halakata. Bhutto ta ce jam’iyar ta, ta Pakistan People’s Party, na kann shawarar kauracewa zaben majalisar da za’a gudanar a watan janairun sabon shekara.