1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Senegal ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe
February 16, 2024

Jami'an tsaron kasar Senegal na murkushe duk wata adawa da soke zabe tare da kashe matasa uku

https://p.dw.com/p/4cVRM
Berlin Tageszeitungen
Hoto: Jens Kalaene/dpa/picture alliance

Jaridar die tageszeitung ta kara da cewa bangaren dan takara Bassirou Diomaye Faye da ke tsare sun sha alwashin ci gaba da gudanar da yakin neman zabe duk da dagewa daga aka yi zuwa watan Disemba. Su ma dalibai a jami'ar Casamance wadanda akasarinsu ke mara wa 'yan adawa baya sun nemi hadin kan sauran takwarorinsu wajen shirya zanga-zangar korar Shugaba Macky Sall daga mulki da zarar wa'adinsa ya kare a ranar 2 ga watan Afrilu. Su kuwa tsofaffin shugabannin kasar Abdou Diouf da Abdoulaye Wade sun goyi bayan tattaunawar kasa da za a gudanar don dinke barakar da ta samu tsakanin 'yan siyasa a Senegal.

Taron kasa  don sulhunta rikicin Senegal
Taron kasa don sulhunta rikicin SenegalHoto: Ngouda Dione/File Photo/REUTERS

Ita kuwa Berliner Zeitung ta yi sharhinta ne kan rikicin Sudan wanda ta danganta da " fagen wakilcin wasu kasashen waje" inda ta ce har a nahiyar Afirka ma dai Rasha na fito na fito da Ukraine a kasar Sudan. Jaridar ta ce rikicin shugabancin Sudan tsakanin sojojin gwamnati da dakarun sa kai ba ya samun sa bakin manyan kasashe na duniya. Amma yana kara zama wani bangare na yaki tsakanin Ukraine da kasar Rasha. A fili yake cewar Ukraine na goyon bayan sojojin kasar Sudan, yayin da sojojin hayan Rasha ke mara wa dakarun RSF baya. Sannan Berliner Zeitung ta kara da cewa ko a taron a karshe da Shugaba Volodymyr Zelensky ya yi da Abdel Fattah al-Burhan ya nuna kusancin da Ukraine ke da shi da mai shugabancin mulkin soja a Sudan.

Shugabannin biyu na son hada gwiwa wajen yakar katsalandan Rasha. Zelensky ya zargi Rasha da jefa Afirka cikin tashin hankali da karancin abinci. Sai dai Rasha ta bayyana Ukraine da Yammacin Turai a matsayin wadanda suka haddasa karancin hatsi da yakin basasa da ke wakana a Sudan. Berlinar zeitung ta ce tasirin Moscow a nahiyar Afirka na dada karuwa. Sai dai  Ukraine na neman ja ma ta birki.

 Assimi Goïta da Abdourahamane Tiani da Ibrahim Traoré
Assimi Goïta da Abdourahamane Tiani da Ibrahim Traoré Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

A bangarenta, Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci kan halin da ake ciki a yankin Sahel, inda ta ce bayan juyin mulkin da kasashen Mali da Burkina Faso suka yi, Jamhuriyar Nijar ma ta hada kai da Rasha. Sai dai ga nahiyar Turai, wannan mataki ne mai matukar hadari. jaridar ta ce Nijar ta hada gwiwa da Mali da Burkina Faso wajen raba gari da ECOWAS ko CEDEAO bayan da suka kafa kungiyarsu ta AES. Sai dai kasashen uku da aka yi juyin mulki a cikinsu na neman abokan hulda a wajen nahiyar Afirka. A ma kokarinta na bin sahun takwarorinsa, firaministan Ali Lamine Zeine ya kai ziyarar kulla dangantaka da Rasha da Chaina da Turkiyya.

Süddeutsche Zeitung ta ce kasashen yammacin duniya na daukar wannan mataki na Nijar a matsayin hadari saboda yana faruwa ne sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro a yankin Sahel, wanda kuma juyin mulki ke kara ta'azzara. Gwamnatocin mulkin sojan sun sanar da cewa za su kawo karshen ta'addanci da kasashensu ke fama da shi ba tare da tallafin sojojin Faransa ba, wanda suka zarga da biyan bukatunsa kawai don kare manufofin Yamma. Amma gaskiyar maganar a cewar jaridar ita ce: burinsu ba zai yi saurin cika ba, ba tare da taimako daga waje ba.