Ta'azzarar rikicin Sudan
July 12, 2023Yakin na Sudan na ci gaba da lalata gine-gine da sauran kayayyakin more rayuwa, gami da cin zarafin dan Adam. A tsawon lokacin rikicin kimanin mutane milyan-biyu da rabi suke tsare daga muhallinsu zuwa wasu wurare a ciki da wajen kasar. A Yammacin Darfur kadai kimanin mutane 180,000 suka tsere zuwa kasar Chadi mai makwabtaka. Ahmed Soliman masani kan kasashe Afirka a cibiyar bincike ta Chatham House da ke binrin London na kasar Birtaniya yana ganin lamura na kara dagulewa ne kawai:
"Bayan shafe watanni biyu da rabi ana fada tsakanin sojoji da mayakan rundunar mayar da martani, inda lamura ke kara sukurkucewa a kasar ta Sudan. An tafka kazamin fada a kewayen birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar da kua yankin Darfur. Sakamakon da yakin ke haifarwa na ci gaba da tagaiyara fararen hula."
A yankin Darfur dai an shafe kimanin shekaru 20 ana rikici mai nasaba da kabilanci. Yunkurin shiga tsakani da kasashen gabashin Afirka na kungiyar IGAD suka yi ya gamu da cikas inda gwamnatin Sudan ta ce za ta shiga tattaunawar idan Kenya ta kawo karshen shugabanci, saboda tana zargi Kenya da tsoma baki kan abin da ke faruwa.
Youssif Izzat mai ba da shawarar siyasa ga Janar Mohamed Hamdan Daglo, Hemeti, na rundunar mayar da martani ya ce abin da suke gudu shi ne kama karya:
"Har yanzu shi Hemeti ya yi imanin cewa hanyar warware matsalar ita ce kadai wajen kaucewa gwamnatin kama karya ko mutum daya ya mamaye harkokin tafiyar da kasa. Muna son samar da tsarin dimukaradiyya da za a girmama, wanda zai kunshi duk 'yan Sudan da samar da adalci. Wannan shi ne batum ba wai a kan wani mutum ba."
Shekara daya da rabi da ya gabata Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kwace madafun ikon kasra ta Sudan tare da nada kansa a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi inda aka kuma nada Janar Mohamed Hamdan Daglo na rundunar mayar da martani a matsayin mataimakinsa, tare da alkawarin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya. Kawo yanzu babu haske kan shirin samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda Ahmed Soliman masani kan kasashe Afirka a cibiyar bincike ta Chatham House da ke binrin London na kasar Birtaniya ke cewa:
"Kawo yanzu duk yunkurin shiga tsakani bai cimma komai ba. Muna da sabon yunkurin tattaunawa a birnin Jedda na kasar Saudiyya da aka samu ci-gaba kalilan kan samar da hanyar shigar da kayayyakin jinkai zuwa kasar ta Sudan."
Ana zargin bangarorin biyu da tarnaki ga duk yunkurin samar da kayyakin agaji ga fararen hula.