Rikicin Sudan ya ja hankalin jaridun Jamus
April 28, 2023Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Sudan, ana kara nuna fargabar cewa rikicin kasar da ke arewa maso gabashin Afirka na iya rikidewa zuwa yaki mai girma. Daruruwan mutane ne aka kashe tare da jikkata dubbai tun bayan barkewar rikicin tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF. Yayin da kasashen duniya, suke ta kwashe jama'arsu mazauna Sudan, har yanzu miliyoyin 'yan Sudan na makale a gidajensu a Khartoum babban birnin kasar da sauran yankunan da ake rikici.
Ita kuwa jaridar die tageszeitung, rikicin Kwango ta duba, tana mai cewa a bisa jadawalin tsagaita wuta da yanzu ake da shi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, 'yan tawayen M23 za su mika ragamar mulki ga rundunar shiga tsakani a yankin. Sannu a hankali mayakan na bacewa daga bainar jama'a, amma kuma suna taruwa a kan tsaunukan kasar. Jagoran kungiyar 'yan tawayen Kwango M23 Bertrand Bisimwa, a halin yanzu yana wani wuri da ba a sani ba a wata kasa mai makwabtaka da Kongo. Yana shirin dawowa Kwango inda zai tafi cikin tsaunukan don haduwa da mayakansa.
Jaridar Süddeutsche Zeitung. Ta ce ficewar kasar Afirka Kudu daga kotun ICC na kwan-gaba, kwan-baya. Shugaba Cyril Ramaphosa yanzu yana son ci gaba da kasancewa a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, a gefe daya kuma ba ya so a kama shugaban Rasha Vladimir Putin. A safiyar Talata ya bayyana a gaban taron 'yan jarida tare da shugaban kasar Finland Sauli Ninistö, wanda ke ziyarar aiki. kuma ya amsa wasu tambayoyi. A bangaren kafafen yada labarai na Afirka ta Kudu, ziyarar da bakin kasashen duniya ke yi a yanzu ita ce hanya daya tilo da za su tambayi shugabansu komai, kusan ya daina gudanar da taron manema labarai da yake yi a baya.
Hukumomi a Kenya sun zakulo mutane 89 da suka mutu daga kungiyar asiri ta mabiyan wata akida. Wanda suka yi imanin da cewa ya kamata mabiya kungiyarsu a Kenya su mutu ta hanyar yunwa. Haka kuma yara ma na cikin wadanda illar kungiyar ta shafa. Shugaban kasar ta Kenya William Ruto, ya yi magana akan abin da ya faru kuma ya kwantata shi da aikin ta'addanci. Adadin wadanda suka mutu a ciki yamutsin wannan kungiyar ya haura yadda ake zato, yayin da masu bincike suka gano karin gawarwaki daga kaburbura a wani daji da ke kusa da gabar tekun kasar ta Kenya.