1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin Sudan na ci gaba da lakume rayuka

Suleiman Babayo MAB
November 8, 2023

Wani kiyasi da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa fiye da mutane 10,000 rikicin Sudan ya kashe yayin da wasu fiye da milyan hudu da rabi suka tsere daga gidajensu.

https://p.dw.com/p/4YaND
Rikicin Sudan
Rikicin SudanHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

'Yan sandan kasar Sudan sun yi amfani da karfi wajen fitar da fararen hula da makarantun da suka samu mafaka sakamakon rikicin da ke faruwa tsakanin sojoji da rundunar mayar da martani a jihar Gedaref da ke gabashin kasar, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar.

Galibin daruruwan mutanen da suka samu mafaka bayan sun tsere daga birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda fada ya yi zafi tsakanin bangarorin na sojoji da kuma rundunar mayar da martani.

Kusan mutane 300,000 suka tsere zuwan jihar ta Gedaref sakamakon rikicin. Wata kungiya mai saka ido kan rikicin na Sudan ta ce fiye da mutane 10,000 suka mutu tun lokacin da rikicin ba Sudan ya balle, sannan wasu fiye da milyan 4 da rabi suka tsere daga gidajensu. Bangarorin da ke rikici a kasar ta Sudan sun gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta yayin zaman taro a kasar Sudiyya.