Rikicin tattalin arziƙin Girka
May 11, 2011Ƙungiyoyin ma'aikata a ƙasar Girka sun sake yin ƙira ga yajin aikin gama-gari a wannan Larabar, domin nuna adawar su da matakan tsuke bakin aljihun da hukumomin ƙasar ke ɗauka da nufin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar. Ana sanya-ran yajin aikin zai janyo dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da kuma ma'aikatu da hukumomin gwamnati - har na tasawon sa'oi 24.
Gwamnatin ƙasar dai ta ragewa ma'aikata albashi da kuɗaɗen fansho, kana ta ƙara kuɗin harajin da take karɓa, a ƙarƙashin wani shirin ɗaukin da ta samu daga ƙungiyar tarayyar Turai da kuma asusun bayar da lamuni a duniya na IMF, wanda ya taimakawa ƙasar tsira daga matsananciyar kariyar tattalin arziƙi kimanin shekara guda kenan.
Wannan yajin aikin ya zo ne a dai dai lokacin da wasu jami'ai daga ƙungiyar tarayyar Turai da kuma asusun na IMF suka isa Athens, babban birnin ƙasar domin nazarin ci gaban da ƙasar ta Girka ta samu cikin watanni huɗun da suka gabata game da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ta. Sakamakon binciken kuɗin da jami'an za su yi ne kuwa zai tantance ko ya dace ta sami kason tallafin kuɗin - na gaba ko kuma neman ta ƙara ɗaukar matakan tsuke bakin aljihun. Ƙasar Girka dai tana ta faɗi-tashin rage yawan giɓin kasafin kuɗin da take samu kuma ana jita-jitar cewar za ta nemi ƙarin taimako nan bada daɗewa ba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu