1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine ya dauki sabon salo

April 14, 2014

An kira taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin kasar Ukraine da yanzu aka yake yaduwa a sassan gabaci kasar.

https://p.dw.com/p/1BhPm
Hoto: Reuters

An gudanar da taron gaggawa na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na kasar Amirka, kan rikicin da ke fauruwa na kasar Ukraine.

Kasar Rasha ta nemi gudanar da taron na gaggawa, bayan Shugaban Ukraine na wucin gadi Oleksander Turchynov ya bayyana daukan matakan yaki da 'yan ta'adda kan masu goyon bayan Rasha, muddun suka ci gaba da mamaye mahimman gine-gine na gabashin kasar.

Jakadiyar Amirka a majalisar Samantha Power ta zargi Rasha da neman dagula lamura a gabashion kasar ta Ukraine. Kasashen Turai sun gabatar da wasu bayanai da ke kutsen Rasha.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal