1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Nana Akufo-Addo ya rage albashinsa

Abdullahi Tanko Bala
March 25, 2022

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da ministocinsa sun rage albashinsu da kashi talatin cikin dari a karkashin matakan rage kashe kudi yayin da kasar ke fama da tsadar makamashi sakamakon rikicin Ukraine.

https://p.dw.com/p/491El
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta ya sanar da cewa an dakatar da dukkan tafiye tafiye zuwa kasashen waje ga masu rike da mukaman gwamnati sai wanda ya zama wajibi. Hakan nan kuma an dakatar da sayo sabbin motoci daga waje ba tare da wani jinkiri ba.

Yace gwamnati na fatan yin tsimin kimanin dala miliyan 400 daga wannan mataki. Sai dai 'yan adawa sun ce matakin bai wadatar ba.

Tashin gwauron zabi na farashin mai a duniya sakamakon yakin Rasha da UKraine ya jawo tsadar rayuwa da na sufuri da kasashen yammacin Afirka wadanda suka hada da kasar Ghana suke jin radadinsa.

Dukkan kasashen da suka cigaba da kuma masu tasowa suna kokarin bullo da matakai domin farfado da tattalin arzikinsu bayan tasirin annobar corona sannan kuma yanzu ga tasirin yakin Rasha da Ukraine ya haifar.