Rikicin 'yan adawa a majalisar Nijar
May 19, 2014'Yan majalisar dokoki na bangaren adawa sun bayyana matsayin su na dakatar da aikin wakillan sabon kwamitin gudanarwar majalisar ne, a cikin wata sanarwar da su ka fitar da safiyar litini, a gaban taron majalisa, a dai dai lokacin da ta soma zamanta domin girka mambobin kwamitin gudanarwar nata da aka zaba su 10.
Dama dai tun a zaman majalisar na ranar assabacin da ta gabata ne bayan da takarar wakilin rukunin kawancan jamiyyun adawa na ARN a kan mukamin mataimaki na biyu na shugaban majalisar dokokin ta ki samun karbuwa a majalisar har so biyu, takwarorinsu na adawa na Jam'iyyar Lumana Afrika a wani mataki na nuna goyan bayansu a garesu su ka janye takarar wakilinsu a mukamin mataimaki na ukku na shugaban majalisar.
Hon Seidu Bkari shugaban rukunin yan majalissar dokoki na jamiyyar adawa ta Lumana Afrika ya bayyan dalillansu na daukar wadannan matakai.
Martanin 'Yan Adawa
To amma da ya ke mayar da martani a kan wannan mataki na 'yan adawa Hon. Dauda Mamadu Marte zabebben mataimaki na farko na shugaban majalisar dokokin Nijar daya daga cikin jagororin jamiyyar PNSD Tarayya mai mulki cewa ya yi matakin 'yan adawar na daga cikin tsarinsu na tauye aikin majalisar amma su kam a shirye su ke su ci gaba da aikin ko da ba wakillan yan adawar.
Sai dai kuma a share daya a daidai loakcin da hukumomin niger su ka tsare wani masanin ilmin dokar tsarin mulki a Nijar Malam Amadu Boubacar Hasan biyo bayan wasu kalammai da ya yi akan kotun tsarin milkin suma yan majalissar dokoki na bangaran yan adawar sun fitar da wata sanarwa inda bayan kawo goyan bayansua gare shi su ka nuna shakkunsu a game da adalcin kotun tsarin milkin a cikin hukunce hukuncen da ta ke bayyanawa a cikin rigingimun da ke hada yan adawar da 'yan majority kamar dai yanda honnorable Mumuni Lamido Hamidu na
bangaran adawar ya yi karin bayani
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinado Abdu Waba