1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya bayan mutuwar Falasdinawa 7

June 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buue
Bayan rasuwar fararen hula da dama na Falasdinu sakamakon hare-haren da bisa ga alamu Isra´ila ce ta kai a Zirin Gaza, babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira da a gudamar da bincike game da musabbabin mutuwar Falasdinawan. Wani kakakin MDD a birnin New York ya ce babban sakataren ya damu matuka dangane da kisan da aka yiwa fararen hular, lokacin da wani jirgin ruwan yakin Isra´ila ya harba rokoki a gabar tekun Zirin Gaza. Falasdinawa 7 ciki har da kananan yara 3 suka rasu sannan wasu da dama suka jikata a wannan hari. Rundunar sojin Isra´ila ta ba da sanarwar cewa zata dakatar da kai hare hare har sai an kammala gudanar da binciken kan wannan al´amari. A halin da ake ciki bangaren dake daukar makami na kungiyar Hamas ta Falasdinawa ´yan gwagwarmaya ta sha alwashin daukar fansa ta hanyar kai sabbin hare haren kan Isra´ila. Wani labarin da muka samu yanzu ya ce Hamas ta harba rokoki daga Zirin Gaza zuwa yankunan Isra´ila dake kusa.