1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqO
Jiragen samam yakin Isra´ila sun kai hari a tsakiyar birnin Beirut a karon farko tun bayan da Isra´ila ta fara kai farmaki a Libanon kwanaki 4 da suka wuce. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce an kai hari akan wata hasumiyar hango abokan gaba da kuma tashar jirgin ruwan birnin. Makamin da aka harba ya lalata tagar gilashin hasumiya amma bai yiwa ginin kansa wata mummunar barna ba. Kimanin shekaru biyu da suka wuce aka gina hasumiyar don ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita. A yau din dai Isra´ila ta tsananta hare haren da take kaiwa Lebanon, inda rahotanni suka nunar da cewa fararen hula 18 sun rasu lokacin da helikoptan yakin Isra´ila ya yi lugudar wuta akan ayarin motoci dauke da mutane dake tserewa daga kudancin Beirut. Bugu da kari a karon Isra´ila ta kuma kai hari kan hedkwatar kungiyar Hamas a Beirut. A wani jawabi da yayi ta gidan telebijin FM Libanon Fuad Siniora ya yi kira ga Amirka da ta tsoma baki don a kawo karshen abin da ya kira yakin da Isra´ila ta kaddamar akan kasarsa.