Rishi Sunak ya zama sabon firaministan Birtaniya
October 25, 2022Shi dai Rishi Sunak da ke zama tsohon ma'aikacin banki kuma tsohon ministan kudi, ya zama firaministan Birtaniyya na farko dan asalin Indiya mai bin addinin Hindu. kuma na farko da ya fito daga tsohuwar kasa da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka. Jagoran mai shekaru 42 da haihuwa, ya kasance shugaban gwamnati mafi karancin shekaru a tarihin kasar Birtaniya.
Amma Rishi Sunak ya yi watsi da zaben gaba da wa'adi ko zaben wuri, wanda jam'iyyar Labour ta nemi a gudanar. Ya hau kan kujerar tafiyar da gwamnatin Birtaniya ne, a wani yanayi na tabarbarewar zamantakewa da aka jima ba a ga irinsa ba a kasar. Sunak ya zama firaministan Birtaniya na biyar cikin shekaru shida, wato lokacin da kasar ta zabi a zaben raba gari da Kungiyar Tarayyar Turai, kuma na uku cikin watanni biyu.