Robert Mugabe: Daga gwarzo zuwa dan kama karya
Mugabe ya jagoranci kifar da mulkin farar fata a Rhodesia, ya bude sabon babi ga kasar. Amma mulkinsa na shekaru 37 ya sauya daga shugabanci na gari zuwa na kama karya da tabarbarewar tattalin arziki.
Kadawar guguwar siyasa
Rayuwar Mugabe a fagen siyasa ta fara cikin shekarun 1960 inda aka kafa kungiyar yaki da mulkin mallaka, wadda ta yaki mulkin tsiraru farar fata. Ya shiga jam'iyyar National Democratic Party ta Joshua Nkomo da ta yi adawa da gwamnatin farar fata. An daure shi shekaru 10, a lokacin ya yi karatu tukuru. Da aka sake shi ya tashi ya zama jagoran rundunar Zimbabwe African National Liberation Army.
Mugabe ya karbi mulki
Bayan yakin shekaru 15 da takunkuman duniya, Mugabe ya tilasta wa gwamnatin Ian Smith tattaunawa, an gudanar da sabon zabe an sami 'yancin kai. An zabe shi Firaminista, ya yi sulhu tsakanin jinsuna da inganta matakan kiwon lafiya da ilimi ga bakar fata masu rinjaye. Amma a cikin shekaru biyu an kashe mutane dubu 20 a fada da masu ta da kayar baya daga tsohon abokin dasawarsa Nkomo.
Kwace filaye
A 1987, Mugabe ya samu karin ikon zartaswa a matsayin shugaban kasa, Nkomo kuma a matsayin mukaddashinsa. A shekarun 1990s kasashen duniya sun mayar da shi saniyar ware saboda janyo wa kasar tabarbarewar tattalin arziki da yin magudin zabe da kwace filin manoma farar fata. Matakin kwace filayen da nufin dadada wa tsoffin mayaka, ya gurgunta fannin noma. A 2002, duniya ta kakaba masa takunkumi.
Keta hakkin dan Adam
A shekaru gommai na 2000, Mugabe ya ci gaba takura wa 'yan Zimbabuwe. A 2005 ya fara shirin lalata unguwannin marasa galihu da ya kira haramtattun unguwanni, matakin da kai tsaye ya shafi mutane dubu 700. Matalauta da dama a birane da kauyukan da ke adawa da mulkin Mugabe, sun rasa muhallansu. Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da matakin.
Liyafa ta kasaita
A lokacin da al'umarsa ke fama da matsananciyar yunwa kasarsa kuma ke durkushewa, Mugabe ya yi ruyawa ta almubazzaranci. A 2015 Mugabe ya shirya liyafar kasaita lokacin cikarsa shekaru 91, ya kashe kudi dalar Amirka miliyan daya, inda aka yanka giwa, abin da 'yan adawa suka kira hauka. A 2015 kasarsa ta koma amfani da dalar Amirka bayan da hauhawar farashi ta wuce mizanin lissafi.
Juyin mulkin soji
A 14 ga watan Nuwamban 2017, sojoji sun karbi iko da kafar watsa labarai ta kasa kana sun sanar cewa an yi wa Mugabe daurin talala a gida. A kwanakin da suka biyo baya, mutane sun bazu kan tituna suna bukatar Mugabe ya yi murabus, suna maraba da sojoji. An goyi bayan mataimakin shugaban kasa na farko Emmerson Mnangagwa a matsayin jagora wanda kuma ya maye gurbin Mugabe mako guda baya.
Rashin koshin lafiya
Bayan faduwar mulkinsa, Mugabe, wanda ya taba ikirarin cea zai yi mulki har sai ya cika shekaru 100 a duniya, gaba daya rashin lafiyarsa ta tabarbare. A ranar 6 ga Satumban 2019, hukumomin Zimbabuwe suka sanar da mutuwarsa a kasar Singapore inda ya je neman magani, saboda ya lalata fannin kiwon lafiyar kasarsa da a da ta taba zama gagarabadau.