Rohani zai sayi jiragen sama a Faransa
January 27, 2016Shugaba Hassan Rohani na Iran zai ya da zango a birnin Paris na Faransa a wani yunkuri na daidaita hulda da kasashen yammacin duniya da suka dage takunkunmin karya tattalin arziki da suka kakaba wa kasarsa. Dama dai ya shafe kwanaki biyu a Italiya inda ya gana da shugaban darikar Katolika ta Duniya Paparoma Francis da kuma mahukuntan kasar ta Italiya ciki kuwa har da Firaminista Mateo Renzi.
Rahoni zai iya amfani da wannan ziyara wajen rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da takwaran aikinsa na Faransa Francois Hollande. Fadar mulki ta Teheran ta rigaya ta bayyana cewar za ta sayi jiragen sama 114 a Faransa. A kasar Italiya ma shugaban na Iran ya rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin cinikayya na miliyan dubu 17 na Euro.
A Ganawarsa da Paparoma Francis, shugaba Hassan Rohani ya taba rawar da Iran za ta iya takawa wajen dakile ayyukan ta'addanci a duniya tare da magance rikice-rikicen da suka addabi yankin Gabas ta Tsakiya.