1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar ta yi bayani a kan Rohingya

May 25, 2020

Kasar Myanmar ta aike wa da kotun Majalisar Dinkin Duniya, cikakken bayani a kan matakan tsare rayuka da kare mutumcin Musulmin Rohingya a kasarta.

https://p.dw.com/p/3cjiC
Myanmar Rohingya gehen nach wochenlanger Irrfahrt an Land
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Rubel

Kotun ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da haka a wannan Litinin. A watan Janairun da ya gabata aka umarci Myanmar da ta dauki matakin kare mutumcin tsirarun Musulmi 'yan Rohingya da aka kwashe shekaru ana zargin gallaza musu.

Tun farko dai kasar Gambiya ce ta shigar da kara a gaban MDD ta na zargin mahukumtan Myanmar da keta dokokin kare mutane daga kisan kare-dangi da duniya ta amince da su tun a shekara ta 1948. A cikin shari'ar alkalai 17 sun amince Myanmar ta dauki matakin dakatar da cin mutumcin Musulmin na Rohingya, kuma sun bukaci Myanmar da ta rinka sanar da su irin matakan da take dauka a duk bayan watanni shida har sai an kammala shari'ar zargin kisan kare-dangin da aka yi wa 'yan kabilar ta Rohingya.