1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rouhani ya gargadi Amirka

May 23, 2020

Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya yi barazanar daukar fansa kan Amirka, muddin ta haddasa tarnaki ga jiragen ruwan da ke dauke da man kasar da suka doshi Venezuela.

https://p.dw.com/p/3cfhH
Iran | Coronavirus: Hassan Rouhani
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/Iranian Presidency

Cikin wata tattauanawar da ya yi ta wayar tarho da Sarkin Katar, Shugaba Rouhanin ya yi wannan gargadi ga Amirka kamar yadda wata kafar watsa labarai ta Mehr ta ruwaito a Iran din.

Wasu jiragen dakon man fetur biyar ne dai a yanzu ke kan hanyar yankin Carribean, inda ake sa ran daya daga cikinsu zai iya isa ruwayen kasar a gobe Lahadi.

A share guda kuwa kasar ta Iran ta sanar da sassauta dokar hana fita saboda corona, tana mai cewa ta bullo da wasu matakan hana yaduwar annobar a wasu larduna uku. Tun a tsakiyar watan Fabrairu ne dai kasar ta sanar da samun mutum na farko da cutar ta kama.