Rowhani na kan gaba a zaben Iran
June 15, 2013Ma'aikatar harkokin cikin gidan Iran ta sanar da cewa Hassan Rowhani na kara samun tagomashi a ci gaba da kirga kuri'un da a ka kada a zaben da a ka gudanar a kasar. Ya zuwa yanzu dai ya samu rinjayen kaso 51 cikin dari na kuri'un da aka kirga daga kaso 65 na tashoshin zabe a kasar. Rowhani dai malami ne mai sassaucin ra'ayi kuma tsohon mai shiga tsakani kan tattauna batun makamashin Nukiliyar Iran.
A jawabin da ya yi shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamnei, ya bayyana cewa za a mutunta zabi 'yan kasa ko da Rowhani ne ya samu rinjayen da a ke bukata. Ya kuma kara da cewa 'yan Iran na da yakini a kan sahihancin zaben da a ka gudanar shekaru 34 bayan juyin-juya hali da a ka yi a kasar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe