RSF ta bukaci Nijar ta sako 'yar jarida da ta kama
October 2, 2023Tun kwanaki biyun da suka gabata ne aka kama Samira Sabou a gidanta, amma kuma har yanzu danginta ba su da labarin inda hukumomin mulkin soja suke tsare da ita.
Sai dai a wani sakon da ta wallafa a kafar sadarwa ta X da aka fi sani da Twitter, RSF ta nemi a bar lauyanta ya gana da ita domin ba ta kariyar da take bukata a fuskar doka.
Da ma dai an taba daure 'yar jarida Samira Sabou a cikin watan Yunin 2020 wato shekaru ukun da suka gabata, a shari'ar da aka yi mata kan bata suna, biyo bayan badakalar cinkin makamai, kafin a sako ta daga bisani. Ba wani ba ne ya yi karar 'yar jaridar illa Sani Mahamadou Issoufou, wato dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou.
Ita dai Samira Sabou ta kasance daya daga cikin 'yan jarida da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke yi wa barazan tun juyin mulkin da ya hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum watanni biyu ke nan a suka gabata.