1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rub da ciki da kuɗaɗen mai da iskar gas a Najeriya

October 25, 2012

Rahoton wani kwamiti da gwamantin Najeriya ta kafa ya yi zargin wawashe ɗaukacin kudin mai da iskar gas ɗin ƙasar a tsakanin 'yan boko da kamfanonin ƙasashen waje.

https://p.dw.com/p/16XI4
Hoto: AP

A wani abun da ka iya kama hanyar kara tada hankalin talakawa da ma masu fatan ganin bayan annobar cin hanci da rashawa a tarrayar Najeriya, wani rahoton wani kwamitin da gwamantin ƙasar ta kafa yayi zargin abun da ya kira wawashe ɗaukacin kudin mai da iskar gas din tarrayar Najeriya a tsakanin 'yan boko da kamfanonin ƙetare.

A cikin ɗan ƙanƙanen lokaci iskar ta kaɗa, haka kuma babu ɓata lokaci zunbutun kazar ne ke neman fitowa a tarrayar Najeriya inda rikicin janye tallafi ke ci-gaba da kaiwa ga bankaɗo mummunan cin hancin da ya mamaye masana'antar man ƙasar na lokaci mai tsawo.

Na farkon fari dai na zaman wani rahoton majalisar wakilan da ya yi nasarar bankaɗo yadda wasu shaffaffun kasar ta Najeriya ke kwasar dubban milliyoyin Nairori a duk shekara da sunan tallafin man fetur ɗin da babu shi.

To sai dai kuma yanzu haka tana shirin kiran ruwa ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da harkar masana'antar sakamakon wani rahoton da ya ce kasar ta yi asarar dallar Amurka milliyan dubu 29 ko kuma abun da ya wuci kasafin kuɗin ƙasar na shekara guda daga wa kaci ka tashin da ta mamaye harkokin man a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Nigeria Nuhu Ribadu Präsidentschaftskandidat
Nuhu Ribadu shugaban kwamitin da ya gabatar da rahotonHoto: AP

Gwamnati ba ta ga kuɗaɗen ba

Ba dai baiwa gwamantin ƙasar ko sisi ba daga ɗimbin arzikin iskar gas ɗin da ƙasar ta riƙa haƙowa ta na kai su ga Turai domin sayarwa.

Sannan kuma shi kansa kamfanin man Najeriya na NNPC ya samu kuɗin da suka kai sama da dallar Amurka milliyan dubu 80 amma kuma sun bi shanun sarki da ma aljihunan wasu shugabaninsa.

Banda kuma damar fitar da man da ma haƙar sa da ake bai wa wasu shafaffu domin tara abun duniya, ko bayan uwa uba karyar da farashin man ga manyan kamfanonin hakar man na ƙasa da ƙasa da suka ɗauki lokaci suna cin karensu babu babbaka da kuma ake ta'allakawa da mugunyar cin hancin masana'antar.

Tuni dai ra'ayi ya banbanta a tsakanin ministar man da ta ce gwamantin na shirin karɓa tare da nazarin rahoton cikin ƙasa da makkoni biyu masu zuwa da kuma jam'iyyar adawar kasar ta Mallam Nuhu Ribadu da ta ce fadar na shirin watsi da shi.

To sai dai kuma ko bayan ita kanta fadar gwamantin dai sabon rahoton daga dukkan alamu ya kama hanyar ta da hankula a tsakanin talakan ƙasar da ya dade yana buga kirjin mallakar arzikin na mai amma kuma ke ci-gaba da wandaka a cikin talauci.

Mafi daukar hankali a cikin rahoton mai shafuka 146 dai na zaman rawar da ake zargin ita kanta ministar man da kuma madugu uban tafiya da takawa ga wani bashin dallar Amurka milliyan dubu ɗaya da rabi da ake bin wani kamfanin waje na Addax da kuma aka ce mai shi ya miƙa na goro don ganin yafe masa sannan kuma ya cefanar da kamfanin ya yi gaba.

Rashin kyakkyawan tsarin shugabanci

Abun kuma da cewar Ezenwata Nwagu dake zaman mataimakin shugaban ƙungiyar "Transparency in Nigeria" mai yaki da cin hanci da rashawa a ƙasar alama ce ta rushewar tsarin shugabancin da ƙasar ke tafiya kai a yanzu haka.

Nigeria Bodo, Ogoniland Öl
Hoto: AP

Mun san masana'antar man Nigeria a cike take da cin hanci, kuma mun san cewar ba wanda zaa gurfanar gaban kuliya kan wannan. Kila kawai abun da kwamitin nuhu ribado yayi mana shine ƙarin adadin da aka sace sanan da kuma kara mana ilimin sanin cewar ɗaukacin masana'antar man ya zama bututu na sace kudin talakan Najeriyar dake neman ganin mulki na gari karkashin demokaraɗiya.

An dai daɗe ana zargin komawar masana'antar man fetur din ƙasar wata kafar wasoso a tsakanin 'yan boko da 'yan siyasar ƙasar. Abun kuma da ake ta'allakawa da gazawar yunƙurin tabbatar da cin gashin kai da kyautatuwar al'amura a cikin harkokinta.

Mawallafi: Ubal Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal