1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Fargaba kan hare-haren Rasha

Suleiman Babayo LMJ
February 24, 2022

Lamura sun dagule a gabashin Ukraine bayan da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bai wa dakarun kasarsa umurnin yin kutse, inda aka shiga yanayin yaki da rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/47XWE
Rikicin Ukraine | Harin Sojojin Rasha
Jiragen yakin Rasha na kara-kaina a wajen Kyiv, fadar gwamnatin UkraineHoto: AP Photo/picture alliance

Yayin wani jawabi Shugaba Vladimir Putin na Rasha da ya kaddamar da kutsenz, ya zargin gwamnati Ukraine da zama ta 'yan makisanci da mutanen da suka gaza kare kasar lokacin yakni duniya na biyu da sojojin Jamus karkashin jagorancin 'yan Nazi suka kaddamar: "Ina magana da sojojin Ukraine. Ku ajiye makamai. Kakanninku da kakannin-kakanninku ba su iya fada da 'yan Nazi ba, saboda kar masu irin wannan ra'ayi su samu madafun iko a Ukraine. Kun yi rantsuwar kare mutanen Ukraine. Masu ra'ayin makisanci sun kwace madafun iko. Suna tatse mutanen Ukraine. Kar ku cika musu burinsu na aikata laifuka. Ku ajiye makamai ku tafi gida."

Karin Bayani: Martanin Turai ga Rasha kan gabashin Ukraine

Rundunar sojan kasar ta Ukraine ta bayyana mutuwar sojojinta fiye da 40, sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin na Rasha suka kaddamar. Rundunar ta kuma musanta ikirarin 'yan aware, na cewa sun karya shingen da sojojin suka yi. Rahotanni daga Kyiv babban birnin kasar ta Ukraine suka nuna cewa, an ji karar wasu abubuwa masu fashewa. Gwamnatin Ukraine din ta katse huldar diflomasiyya da Rasha, kamar yadda Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya bayyana: "Mun katse huldar diflomasiyya da kasar Rasha. Kuma kasar Ukraine za ta kare kanta, ba za ta mika wuya kan 'yancinta ba ko wane irin tunani mahukuntan Moscow ke da shi."

Rikicin Ukraine | Shugaba Volodymyr Zelenskyy
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr ZelenskyyHoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP Photo/picture alliance

Ukraine din dai ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin dakatar da Shugaba Vladimir Putin na Rasha kan kutsen. A nasa bangaren, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar António Guterres ya nemi ganin kawo karshen lamarin da ke kara rincabewa: "Ina da abu guda daga zuciyata. Shugaba Putin ka dakatar da dakarunka daga kai hari Ukraine. A bai wa zaman lafiya dama. Mutanen da dama sun riga sun halaka."

Karin Bayani: Takaddama tsakanin Rasha daTurai

Tuni dai kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN ta kira taron gaggawa kan halin da ake ciki, bayan Rashan ta kaddamar da kutsen kan Ukraine. Ita ma dai kungiyar kasashen Tarayyar Turai, ta yi kakkausan suka kan matakin na Rasha. Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen ta nuna takaici, dangane da abin da ke faruwa. A nasa bangaren, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce, lokaci zai nuna irin mummunan kuskaren da shugaban kasar Rashan ya yi. Kawo yanzu sojojin Ukraine sun dakatar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwan kasar, amma an ci gaba da sufurin jiragen kasa.