1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin makoma kan tsawaita wa'adin Naira

February 10, 2023

Majalisar zartarwar Najeriya ta ce tana goyon bayan shirin sauya kudin kasar duk da kalubalen da yake fuskanta a yanzu.

https://p.dw.com/p/4NLsO
Sabbin takardun NairaHoto: Ubale Musa/DW

Ya zuwa ranar wannan Juma'ar dai wa'adin babban banki na kasar na daina amfani da sabon kudin ke karewa, kuma daukaci na hankali na 'yan kasar ya koma ya zuwa zauren taron majalisar magabata ta kasar da nufin sanin mataki na gaba a cikin tarayyar Najeriya in da kusan kowa ke zaune cikin rudani.

Majalisar da ke zaman mafi girma a kasar dai ta kammala taronta tare da amincewa da ci gaba da aiwatar da manufar da 'yan majalisar suka ce tana da tasiri ga kokari na sauya da dama cikin kasar.

Nigeria | Präsident Muhammadu Buhari | Einführungszeremonie für neu gestaltete Banknoten
Buhari lokacin kaddamar da Naira Hoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

Majalisar dai ta nemi babban banki na kasar ya kara yawan kudaden da yake samarwa tare da fitar da karin takardu na kudin Naira 100, da 50 da 20 da ma 10 da Naira biyar domin amfanin al'umma.

Koma ta ina ake shirin abi a cikin kaiwa ya zuwa mafita dai, babu wata sanarwa bayan kare wa'adin babban banki na kasar.

Abubakar Malami dai ya ce gwamnatin kasar na shirin bin umarnin kotun kolin, har ya zuwa Larabar da ke tafe da kotun take shirin dora wa bisa shari'ar .

Koma ya take shirin kayawa a cikin kotun daga dukkan alamu dai rikicin sabo na kudin na dada kara fitowa fili da irin girman rabuwar da ke tsakani na jami'ai na gwamnatin APC 'yar mulki.

Öl Globaler Einfluss Geld Finanzen Nigeria Naira
Tsoffin takardun NairaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

An dai daya daga cikin gwamnonin ya fito cikin zauren taron rai baci yana ta korafin hanasu damar fadi aji ko ba dadi a cikin zauren taron

Su kansu majalisun tarayyar kasar guda biyu dai basu boye adawarsu bisa sabon matsayin majalisar magabata na kasar ba.

Shugaban majalisar dattawa na kasar Senata Ahmed lawal da ya jagoranci wata ganawa da shugaban kasar bayan taron dai ya ce basa goyon bayan neman kaiyyade lokaci na sauya kudaden.