SiyasaSpaniya
Rudun siyasa a Spain
September 27, 2023Talla
Alberto Nunez Feijoo wanda jam'iyarsa ta People Party ta samu rinjaye a zaben da ya gabata ya yi fatan zama firimiyan Spain, amma kuma a wannan larabar sai ya gaza samun kuri'u da yake bukata daga 'yan majalisar dokoki. Yanzu dai bisa dokokar kundin tsarin mulkin kasar Spain, Feijoo na iya neman zama firaminista karo a na biyu a zauren majalisar dokonkin kasar, inda in ya samu karamin rinjaye hakan na iya ba shi damar darewar kujerar firimiyar kasar. Idan dai har a ranar Juma'a karo na biyu Feijoo bai samu nasara ba, to ya zama tilas wa Pedro Sanchez mai rikon kwaryan kujerar firaminista a yanzu, ya tattauna da jam'yar masu neman ballewa ta al'ummar Catalan domin samun kafa gwamnatin hadaka.