Ruguguwar cire kudi a bankunan Kasar Girka
June 19, 2015A Kasar Girka a daidai lokacin da ya rage mako daya wa'adin da Kasar ta ke da domin biyan kudadan bashin da ake biyar ta,al'ummar kasar masu ajiyar kudade a bankuna na cigaba da yin tururuwa zuwa bankunan domin kwashe kudadan ajiyarsu.Wata cibiyar bayar da bayanai kan harakokin tattalin arziki ta Kasashen Turai ta kiyasta cewa kimanin kudi miliyon dubu ne na Euro mutanen suka cire daga bakunan kasar a ranar Alhamis kadai.
A ranar Litanin mai zuwa ne dai shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ke gudanar da zaman da ake yiwa kallon tamkar na sa'ar karshe ga shawo kan matsalar bashin kudin Kasar ta Girka.Sai dai kwararru a fannin harakokin kudi dama Kasashen Turai da dama na ganin da wuya taron na ranar litanin ya iya kai wa ga shawo kan matsalar.Amma gwamnatin Kasar ta Girka na cewa ita kam ba ta yanke kauna ba a game da yiwuwar gano bakin zaren matsalar a wannan taron koli.