Rukunan gasar cin kofin duniya 2022
April 1, 2022Mai masaukin baki Katar ta fada a rukuni na A wato rukuni daya da kasashen Ecuador da Senegal da kuma Netherlands. Kasar Ghana da ta fitar da Najeriya daga shiga gasar ta na rukuni na H inda za ta kece raini da kasashen Portugal da Uruguay da Koriya ta kudu.
Kasar Jamus kuwa ta fada ne a rukuni na E inda anan ma kasashen Spain da New Zealand da Japan suka fada. Ita kuwa Ingila ta fafata da kasashen Iran da Amirka da kuma Ukraine a rukuni na B. A taron raba rukunan da ya gudana a birnin Doha na kasar Katar kasar Faransa da ta lashe gasar da ta gabata ta fada a rukuni na D da kasashen Hadaddiyar daular larabawa da Denmark da kuma Tunusiya.
Za a dai a fara gudanar da gasar ne a ranar 21 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2022 a birnin Doha na kasar Katar.