Fashewar makamai ya kashe mutane a Siriya
August 12, 2018Talla
Kungiyar kare hakkin bil'a Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce ana ci gaba da tsamo gawarwakin mutane da ke makale a karkashin baraguzan gini. Rahotanni na cewar yawancin wadanda suka mutun na da alaka da mayakan kungiyar Tahrir al-Sham da ta yi alaka da kungiyar 'yan jihadin kasar Siriya a shekarun baya. Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tarwatsewar wurin adana makaman ba, sai dai a baya-baya nan dakarun gwamnatin Siriya sun zafafa kai hare-hare da bama-bamai a kudancin Idlib a wani mataki na kwashe yankunan a hannun 'yan awaren gwamnati.